''Duk shaidun da suka gabatar a gaban kotu shaidu ne wanda kotu bata gamsu da ita ba domin duk lokacin da lauyoyin APC suka gabatar da shaida mukan tabbatarwa da kotu cewa wannan ba shaida bane wanda kotu zata saurari abunda ya bayyana a gabanta wanda ya sani domin duk ƙarshen tambaya sai mun tabbatarwa da kotun da shaidar cewa ba sunan sa jam'iyyar APC ta tura domin wakiltar ta a INEC ko kuma akwatun da suke iƙirarin sunyi aiki a kansa ba kuma har suke zargin anyi aringizon ƙuri'u a ciki ba. Don duk cikin su babu wanda ya iya tabbatarwa da kotu cewa shine Agent na akwatun da yake zargin anyi aringizon ƙuri'u a kai don babu wanda ya iya maimaita sa hannun wato signature dake kan takardar tattara sakamako ta INEC.'' inji lauyan NNPP
Barr. Bashir Yusuf Tudun Wuzurci ya bayyanawa manema labarai cewa INEC ta ƙi kawo shaida ne saboda babu wata hujja da aka kawo da zasu kare saboda haka da yiwuwar NNPP ma taƙi kawo kowace Hujja domin basu da abunda zasu kare a gaban kotu kasancewar shaidun APC su tabatarwa da Kotu cewa ba da gaske suke ba kuma wasa ƙwaƙwalwa kawai ake a tsakanin su.