Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) a ranar Talata ta ce za ta gurfanar da wasu da ake zargi da aikata laifukan da suka jiɓanci zaben 2023 a gaban kotu.
Hukumar ta ce mutanen da za ta gurfanar kan irin waɗannan laifuka sun kai 215 daga ɓangarori daban-daban na kasar.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga daukacin kwamishinonin zabe a babban ofishin hukumar da ke Abuja.
Ya kara da cewa hukumar zabe za ta hada hannu da kungiyar lauyoyin Najeriya NBA wadda a cewarsa a shirye take ta gurfanar da masu laifin a gaban kotu ba tare da an biya komai ba.
“Dole ne mu yarda cewa akwai wasu ƙalubale - wasu na rashin kayan aiki, wasu na rashin isassun ma'aikata. Muna duba bayanan wadanda suka aikata laifuka,” in ji Yakubu.
“Akwai kararraki 215 daga ‘yan sanda kan laifukan zabe, muna aiki tare da NBA don gurfanar da masu laifi. Tuni Hukumar NBA ta gabatar da jerin sunayen lauyoyi 427 wadanda a shirye suke su gurfanar da wadancan kararrakin kyauta.”
Da yake nazarin zabukan, Yakubu ya ce zabukan 2023 sun samu kyakkyawan idan aka kwatanta da zabukan da aka gudanar a baya.