Likitocin Najeriya da ke aiki a asibitocin gwamnati sun bai wa gwamnatin kasar wa'adin mako biyu ta cika musu alkawuran da ta daukar musu a jarjejeniya da suka cimma a baya.
Gwamnatin da ta shude ce dai ta alkawarta warware duka matsalolin da kungiyar bayan yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da likitocin suka yi a watan Mayu, to amma kungiyar ta ce babu abin da aka yi game da cika musu alkawari tun bayan da tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki.
A cikin wata sanarwa da kungiyar likitocin Najeriya NARD ta fitar, ta ce ta yi imanin cewa wa'adin mako biyu ya isa hukumomi su magance mata matsalolinta.
Matakin na zuwa ne, wata guda bayan da likitocin suka ce za su bai wa sabuwar gwamnati lokaci domin duba lamarin.
Wasu daga cikin bukatunsu sun hada da ƙarin kashi 200 na albashinsu, da biyan su wasu kukakde da suka ce suna bin gwamnati, da kudin horarwa, da batun cike gurbin ma'aikata da suka bar aiki, domin magance ''matsalar karancin likitoci a asibitocin kasar''.
Ƙungiyar ta yi gargadin cewa matukar aka kasa biya mata bukatunta zuwa ranar 19 ga watan Yulin da muke ciki, "Fannin kiwon lafiyar kasar zai sake shiga wani hali" a fadin ƙasar.
Rashin isassun kuÉ—aÉ—e, da rashin isassun kayan aiki da karancin albashin ma’aikatan kiwon lafiya ya sa kwararrun likitoci da dama na neman ayyuka a Æ™asashen waje.