Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa kwamishinonsa cewa za a tantance su bayan wata shida da kama aiki domin sanin waÉ—anda za su ci gaba da aiki da kuma waÉ—anda za a kora.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da majalisar zartarwar jihar ta yi zamanta na farko a yau Laraba.
A cikin jawabin da ya gabatar, Abba ya ce "Ina tunatar da ku cewa kuna da wata shida na gwaji bayan naɗa ku kan muƙami, bayan haka ne za a duba ayyukan da kowace ma'aikata ta gudanar, za a yaba wa waɗanda suka yi ƙoƙari sannan za a yi waje da waɗanda ba su yi ƙoƙari ba."