Joel Oruche, Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin 17 ga Yuli, 2023.
Tabbatar da hakan na zuwa ne bayan da aka gano alamun cutar a wata gona da ke Gajiri, kusa da babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, a karamar hukumar Suleja, jihar Neja.
Sakamakon gwajin da Cibiyar Nazarin Dabbobi ta Kasa (NVRI) ta gudanar -Vom, jihar Filato ta tabbatar da bullar cutar a ranar 16 ga Yuli, 2023.
Wannan bullar cutar a baya-bayan nan ta biyo bayan sanarwar da gwamnatin Najeriyar ta yi inda ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi taka tsantsan saboda barkewar cutar Anthrax a makwabciyarta Ghana makonnin da suka gabata.
Gwamnatin Najeriya da gwamnatin jihar Neja sun dauki matakin dakile yaduwar cutar.
An sanya gonakin da abin ya shafa karkashin keɓe, kuma an raba allurai 50,000 na rigakafin cutar anthrax. An kafa kamfen na wayar da kan jama'a da sauran matakan kariya don shawo kan yaduwar cutar.
Anthrax cutar dabbobi ne da ake kamuwa da ita ta hanyar ƙwayoyin cutar ta iska.
Da farko yana shafar dabbobi kamar shanu, tumaki, da awaki, amma kuma mutane na iya kamuwa da cutar idan suka yi hulɗa kai tsaye da dabbobin da suka kamu da cutar ko kuma suka cinye kayayyakin da suka kamu da cutar.
Alamomin cutar Anthrax a cikin dabbobi sun haɗa da mutuwa kwatsam da zubar jini daga hanci da baki, da dubura.
Ƙwayoyin cutar na Anthrax suna bunƙasa ne yawanci a cikin gurɓataccen wurare..
Gwamnati na karfafa masu dabbobi, manoma, da jama'a da su sanya ido tare da kai rahoton duk wani lamari da ake zargi.