Mai magana da yawun shugaban ƙasar Dele Alake, ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja.
Shugaban ƙasar ya bayar da umarnin mayar da duka al'amuran da suka shafi samar da abinci da ruwan sha, a matsayin manyan abubuwan dogaron rayuwa zuwa ƙarƙashin kulawar majalisar tsaro ta ƙasa.
Alake ya ce umarnin na cikin tsare-tsaren gwamnatin Tinubu na tabbatar da tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar.
Ya ce Shugaban ya damu kan yadda farashin kayan abinci ke ƙaruwa da yadda hakan ke shafar talakawan ƙasar.
Shugaban ya kuma bayar da umarnin gaggauta bai wa manoman ƙasar taki da irin shuka domin rage musu raɗadin cire tallafin man fetur.
Ya Æ™ara da cewa “Dole hukumomin ayyukan gona da ta ruwan sha su yi aiki tare domin tabbatar da ingantuwar noman rani a Æ™asar don tabbatar da samar wadataccen abinci a Æ™asar a kowanne yanayin shekara''.