Bayanin ya nuna cewa an samu mutuwar kashi 17.2 cikin ɗari na waɗanda suka kamu da cutar, wanda ya yi ƙasa adadin waɗanda suka mutu bayan kamuwa da cutar a cikin irin wannann lokacin 2022 mai kashi 19.6 cikin ɗari.
Wannan na kunshe ne a cikin sabon rahoton mako na 25 zuwa na 27 kan bullar cutar zazzabin Lassa a Najeriya wanda NCDC ta wallafa a ranar Litinin.
Hukumar NCDC ta kuma bayyana cewa kashi 73 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar zazzabin Lassa sun fito ne daga jihohin uku (Ondo da Edo da kuma Bauchi) yayin da kashi 27 cikin 100 kuma daga jihohi 25.
A cikin kashi 73 cikin 100 da aka tabbatar sun kamu da cutar, Ondo ta samu kashi 33 da Edo kashi 29 sai kuma Bauchi kashi 11.