A cikin wata sanarwa da ta fitar, bayan kammala taron shugabanninta na ƙasa, ƙungiyar ta 'Association of Master Bakers and Caterers of Nigeria' ta ce ta ɗauki matakin ne bayan la'akari da nunnukawar farashin kayan aiki.
Sanarwar wadda ta samu sa hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Mansur Umar ta ce tashin farashin ya biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tarayya ta yi.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a cikin jawabinsa na karɓar mulki.
Lamarin ya haifar da tashin litar man fetur daga kimanin naira 200 zuwa sama da naira 500 a faɗin ƙasar, wani abu da ya haifar da tashin farashin sufuri da kayan masarufi.
Ƙungiyar ta ce abubuwan da take amfani da su wajen gudanar da sana'ar, waɗanda suka haɗa da man fetur, da gas, da fulawa, da suga da sauran su duk sun yi tashin gwauron zabi.
Haka nan ƙungiyar ta koka kan yadda hukumomi daban-daban a ƙasar ke karɓar haraji, kala-kala, wani abu da ke ƙara saka masu gidajen burodin cikin matsi.
Kan haka ne ta ce "An umurci dukkanin shugabannin ƙungiyar na yanki su tabbatar cewa ƴaƴan ƙungiyar sun bi wannan umarni, har sai idan sun samu wani sabon umarnin daga uwar ƙungiyar ta ƙasa."