Hon Dr Zakariyya yakuma kara da cewar bashi da burin daya wuce yaga yankin kura/garun malam sunzama madobin Jihar Kano, musamman inda yake fata yaga yankunan sunfarfado wajen gannin sundawo da kanbunsu na Noma.
Inda yace bangaren Noma yana fatan kura/garun malam su ciyar da kano da abinci dama najeriya, "Noma shine asalinmu kuma zamu farfado da Noma domin yankinmu yazamana shine hedkwata din Noma mai girma Hon a najeriya da makwabtanmu ana yi mana take wajen noman shinkafa, wacce shinkafa irin tamu al'umma suna matukar santa.
Ina mai tabbatar maka da cewar zamu farfado da Noma a wannan yankin, dan majalissa wakilin al'umma ne aikin mu shine kai kudiri wajen gwamnati, to bazamuyi kasa a gwiwaba wajen kai kokenku ga gwamnati, kuma nasarar mu bawai iya nasarar NNPP bace a'a nasarar dukkan al'ummar da muke wakilta ne.
Daga sanda mukaci zabe mukabar maganar wannan dan jam'iyyar kazane hakkinsu duka yana wuyanmu, muna fatan za'a cigaba da tayamu da addu'a da shawarwari wajen gannin munsauke nauyin da Allah yadora mana".
Anashi jawabin shugaban jam'iyyar ya nuna farincikisa da wannan ziyarar "tabbas munsan kuncancanchi jagoracin wadannan yankuna a don haka bazamu gajiya ba wajen yimuku addu'oi da baku duk wata gudunmawar data dace mubaku kofarmu a bude take, muna godiya Allah yacigaba da shiga lamuranku kuma Allah ya maimaita mana Ameen".