Cikin ziyararsa ta barka da babbar sallah ya ziyarci rundunar yansandan Kano reshen yankin da yake wakilta, a jawabinsa na marhabun DPO yankin ya nuna gamsuwarsa da wannan ziyara, yakuma tabbatar da cewar hukumarsa zata bada duk wata gudunmawar data dace don gannin ansamu ingantacen zaman lafiya a Kura/Garun Malam,
Hon Dr Zakariyya Alhassan yayi kira da mazauna yankunan kura/garun malam musamman ma matasa da su zauna lafiya, a cewarsa zaman lafiya shine jigon cigaba a kowacce al'umma, Inda yace hadin kan matasa shine shine zaiciyar da al'umma gaba.