Shugaban kungiyar, Smart Olugbeko, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ya ce mambobin kungiyar ba za su iya ci gaba da rayuwa a kan mafi karancin albashin su ba.
Ya ce umarnin ya biyo bayan babban taron kungiyar da aka yi a ranar Talata, 18 ga Yuli, 2023.
Olugbeko ya ce mambobin kungiyar ba za su koma bakin aikinsu na zuwa kullum ba har sai gwamnatin tarayya ta amince da bukatar COEASU na karin kashi 200 na albashi.