Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta kyale shi ya nemo karin fiye da dala miliyan dari biyar don samar da tallafi a wani mataki na rage radadin cire tallafin man fetur.
Cikin wata wasika da ya aike wa majalisar wakilan kasar, shugaban ya bukaci 'yan majalisar da su yi wa kasafin kudin 2022 kwaskwarima don ba shi damar samo kudin.
Shugaban majalisar Tajudden Abbas, ya karanta wasikar a yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
Abin da wasikar ta kunsa shi ne akwai kudin a kasa, to amma shugaba Tinubun na fatan majalisar za ta gaggauta amincewa da wannan bukata sa.
Shugaban majalisar ya sanar da cewa za a duba wannan bukata a ranar Alhamis.
A shekarar da ta wuce ne tsohon shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya gabatar da batun samar da dala biliyan daya don gudanar da manyan ayyuka a wani kwarya-kwaryar kasafin kudi da ya gabatar.
Dillan man fetur sun kara farashin man fetur da akalla dala daya kan kowacce lita a duk sassan Najeriya bayan Tinubun ya sanar da cire tallafin man fetur a yayin jawabin da ya gabatar a ranar da aka rantsar da shi.