Cikin wata sanawar da hukumar Alhazan Najeriya NAHCON ta fitar, ta ce tana so ta kwantar wa Alhazan da iyalansu hankali.
Domin kuwa dakatarwar da hukumar kula da sufurin jirgin sama ta ƙasar ta yi wa kamfanin ya shafi jigilar cikin gida ne, ba abin da ya shafi jigila tsakanin kasashe ba ne.
Hukumar kula da sufurin jirgin sama ta Najeriya NCAA dai ta ce ta dauki matakin ne saboda wasu al'amura da suka faru da jiragen Max Air ƙirar B737, ciki har da lalacewar wilin tayar saukar jirgin ta gaba, da ta janyo wani mummunan al'amari ga jirgin Boeing 737-400 tsakanin tashinsa daga filin jirgin sama a jihar Adamawa zuwa saukarsa a filin jirgin Nnamdi Azikiwe a Abuja ranar 7 ga Mayu, 2023.
Hukumar Alhazan ta ce tana mai tabbatar wa al'ummar ƙasar cewa dakatarwar ba za ta shafi jigilar alhazan ƙasar da ke gudana ba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa kamfanin zai tabbatar da kwaso duka alhazan da aka ware masa domin yin jigilarsu.
''Muna son gode wa duka 'yan ƙasar da Alhazan dangane da hakuri da juriya da suke nunawa, kuma muna masu tabbatar da cewa za a kammala kwaso mahajjatan ƙasar a kan lokaci kamar yadda aka tsara'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Tuni dai hukumar Alhazan ƙasar ta soma jigilar mahajjatan ƙasar daga Saudiyya zuwa Najeriya