Hukumar ƴan sandan Najeriya ta janye jami'anta na kwantar da tarzoma waɗanda ke aikin kare wasu tsofaffin jami'an gwamnatin ƙasar ciki har da mai ɗakin tsohon shugaban Najeriya Aisha Buhari da Mallam Mamman Daura da tsohon ministan ƴan sanda, Maigari Dingyadi.
Sauran mutanen da abin ya shafa sun haÉ—a da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da Iyorchia Ayu, tsohon shugaban majalisar dattawa.
Gidan talabijin na Channels wanda ya ruwaito wata sanarwa daga hedkwatar rundunar ƴan sandan ƙasar tana cewa umarnin ya fara aiki nan take.
A cewar hukumomin, wannan matakin na zuwa ne a ci gaba da tantancewa da sake tsara bayanan tsaro da rundunar ‘yan sandan Najeriya ke yi.
Hakan kuma na da nufin inganta jami'an 'yan sanda da ake aike wa da kuma tabbatar da yin amfani da kayan aiki yadda ya kamata don shawo kan kalubalen tsaro da ake fama da shi a ƙasar.