Yau ne aka cika shekara 20 da cimma yarjejeniya kasashen Afirka ta kiyayewa da kuma yaki da rashawa.
Babbar sakatariya a kungiyar ta Amnesty, Agnes Callamard, ta ce "Irin halin da masu fallasa rashawa ke shiga a kasashen yammaci da tsakiyar Afirka abin babu dadi, wadannan mutanen fa mutane ne da ke taka muhimmiyar rawa da sadaukarwa wajen yaki da cin hanci da rashawa, to amma sai kaga daga karshe su ake kai wa hari ko wulakanta su saboda kawai sun bayyana gaskiya."
Ta ci gaba da cewa," Dole ne gwamnatoci su tashi tsaye wajen kare hakkin dan'adam da girmama masu kwarmata irin waÉ—annan bayanai da ma biya musu dukkan bukatunsu saboda rawar da suke takawa wajen bayyana marassa gaskiya."