Kwalejin karatu da zana jarabawar share fagge jami'a ta kano wato KCEPS ta samu cigaba ƙarƙashin jagorancin mu tun daga shekarar 2017 har izuwa wannan lokaci da muke kan jagoranci ~ Ass. Prof. Sunusi Ahmad Yakubu
"Lokacin da maigirma tsohon Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kira ni domin tantance ni sai da ya tambaye ni ta yadda za'a ciyar da wannan kwaleji gaba, na faɗa masa irin kudirce-ƙudurcen da nake dashi idan da za'a bamu dama na jagoranci wannan kwaleji mai albarka wanda suka haɗar da : abunda ake kira consolidation wato ɗorawa daga inda magabata suka tsaya, magabatan wanda suka kama tun daga kan (Malam Sa,eedu Gwarzo dattijon arziƙi, Prof. Ibrahim Umar tun yana Dr., Marigayi Mal. Abubakar Imam, Mal. Abdulhamid Hassan, Mal. Tijjani Ibrahim, AT Abdullahi, Saeedu Zakari garun babba, Dr. Kabir wanda ya taba riƙe muƙamin Head of Service, har izuwa Prof. Sani Lawan Malumfashi wanda na gada). Duka waɗannan mutane ne da sukai aiki tuƙuru wajen ganin makarantar ta cigaba. lokacin dana karbi jagorancin sai nabi duk irin abubuwan da suka shiryawa wannan makaranta wanda zai kawo mata cigaba duk muka bi muka bi muka ɗauke daga ciki mun gaji shirin yadda za'a dunga NCE tun daga farko har ƙarshe wanda kafin muzo idan aka fara ba'a gamawa ake fita kuma dokar ta tun ta lokacin soja tun shekarar 1987 itace har izuwa lokacin da muka karbi jagoranci, daga baya muka duba yiwuwar canza shi bayan mun samu sahalewar maigirma gwamnan jihar kano. Daga cikin dokar da muka ƙirƙiro shine: canza mata tsari ta tashi daga CAS zuwa KCEPS wanda dalilin kafuwar dokar ne yasa aka samar mana da mataimaka biyu wanda ya haɗar da DEPUTY PROVOST NCE, da DEPUTY PROVOST CEC. Wannan yana daga cikin cigaban da muka gada wanda baa yi ba da zuwan mu kuma Allah yasa akai wanda ba don an canza sunan ba da bamu samu damar bada halsataccen shedar kammala karatu na NCE ba Alhamdulillah!
'ABU NA BIYU NA CIGABA DA MUKA KAWO A KWALEJIN KARATU TA KCEPS'.
Akwai batun cike gurbi na abubuwan da aka rasa yi a baya wanda tun shekaru hamsin a baya ya kamata a cike amma ba'a cike ba, saboda haka abunda mukai a farlo na canza fasalin tsarin dokar kwalejin da canza mata suna shine abunda ya cike wannan gurbi da aka bari a baya ba'a samu damar yi ba sai a lokacin mu. Tun 1972 da aka kafa wannan makaranta wanda babu wadda ta girme ta har izuwa yanzu wanda daga baya ne aka samu Sa'adatu Rimi, da sauran jami'o'i. Kwalejin ta yaye manya-manyan mutane a Najeriya wanda daga cikin su akwai : tsohon Gwamnan Jihar kano, Sen. Kabiru Ibrahim Gaya,tsohon kakakin majalisar tarayya Rt. Hon. Gali Umar Na'abba, tsohon kakakin jihar kano, tsohon Gwamnan Jigawa Ali Sa'adu Birnin Kudu, shugaban DSS na ƙasa Magaji Bichi da sauran su.
Duk da waɗannan manyan data yaye amma sai ta zama koma baya wajen samun sabbin gine-gine da sauran su, saboda haka sai muka nemi tettfund kan ta shigo domin samar mana da gine-gine masu amfani kuma mukai sa'a suka shigo aka samaf mana da gine-gine mabanbanta kuma daga nan an cigaba daga nan har ƙarshen tettdund sai dai idan jihar kano ce ta dakatar dasu.
CIGABAN DA MALAMAI SUKA SAMU TUN LOKACIN DA MUKA KARBI JAGORANCIN WANNAN KWALEJI TA KCEPS.
A lokacin da muka samu damar jagoranci har izuwa yanzu munyi ƙoƙarin ganin an tura malamai ƙaro karatu a ƙasashen ƙetare wanda har izuwa yanzu akwai wadda take a can ƙasar waje take ƙoƙarin kammalawa kwanan nan kuma muna tattauna yadda zata ƙulla mana ƙwaƙwƙwarar alaƙa tsakanin mu dasu. Munga cigaba ƙwarai da gaske daga waɗannan malamai da muk tura ƙasashen ƙetare inda izuwa yanzu sun fara kawo mana sabbin hanyoyin cigaba a makarantar wanda suka haɗar da Mal. Ahmad Garba Jibri, irin su Mal. Ɗahiru. Sannan wanda suke karatu locally a nan gida wanda a baya malami ba zai samu sama da dubu sittin ba, amma yanzu idan Masters Art Malami yake yi...zai samu 1.2Million wanda shine mafi ƙaranci idan kuwa Science Malami yake yi zai samu 1.5Million idan PHD Art Malami ya tafi zai samu 3.6Million idan kuwa Science yake yi zai samu 4.5Million. Wannan duka an samu wannan cigaba ne ƙarƙashin jagorancin mu a wannan kwaleji mai albarka. A alƙaluman da muka lissafa wanda malamai suka samu wannan tagomashi sun kai kimanin mutum hamsin. A baya mutanen mu basa iya zuwa Conference amma yanzu an samu sama da mutum hamsin sun je Conference kusan ashirin da ɗoriya sun je jihar Lagos sunyi course ɗin da ake kira ASCON wanda da sai dai Gwamnatin jiha ta gayyato su suzo suyi amma ƙarƙashin jagorancin mu mun bada da aka tafi Lagos akai kwana biyar wanda a cikin malaman akwai wanda na san basu taba wuce jihar Kaduna ba amma sun samu damar haure Arewa har zuwa kudancin Najeriya, Kuma wannan yanzu aka fara. Akwai tsarin da aka fito dashi TRAIN THE TRAINER wanda da yawa sun fita ƙasashen waje sanadiyar wannan shiri ciki har da ƙasar Amurka.
Yanzu haka mun samu damar shigo da sabuwar hanyar E- Facilities wanda ɗalibai zasu samu damar hawa na'ura mai ƙwaƙwalwa domin gudanar da karatuttukan su. An bamu dama na samun ƙarin gini wanda ake kira ANNEX daga gefwn makaranta mun samu na kasancewa masu lura da harkokin gudanarwa na sakandiren COMMERCIAL kamar yadda yake bisa tsari doka na kwalejin karatu. Bayan nan mun hango cewa tunda mun samu gabatar manyan mutane daga kwalejin kuma rayuwa tayi tsada wanda da yawa suna son yin IJMB wanda suke zaune a karkara amma basu da dama sai muka duba muka nemi alfarma aka bamu (AMANA COLLEGE) dake ƘUNCHI ta zama ƙarin gurbin karatu na Kwalejin KCEPS a nan muka kai gidan ɗalibai wanda a ƙalla yana cin sama da mutume 360 yanzu haka muna da ɗalibai kusan ɗari suna (NCE PROGRAMME).
Wannan munyi shi ne duba da muka ga hankalin matasa ya karkata wajen smun sana'ar hannu muna ta tunanin idan za muyi amfani da wannan wajen musamman bangaren kekuna na ɗinki wanda za'a dunga koyar da ɗalibai ɗinki duk ƙarshen mako inda zamu nemi sa hannun Gwamnatin jiha da ƙaramar hukuma mafi kusa ta yadda za'a dunga koyar da matasa musamman wanda basu da kwalin karatu ɗinki dama yadda zasu dunga kaiwa kasuwa suna siyarwa...
Muna da tabbacin wannan gwamnati mai ci zata bamu gudunmawa mai ƙarfi wannan harka ta matasa duba da cewa gwamnatin tasu ce kuma yana ɗaya daga cikin jadawalin shine: inganta rayuwar matasa ta hanyar basu ilimi da abun dogaro dakai''.
KASO NA BIYU NA WANNAN ƘAYATACCIYAR HIRA TARE DA SHUGABAN KWALEJIN KARATU TA KCEPS ASS. PROF. SUNUSI AHMAD YAKUBU NA NAN ZUWA.