A wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta fitar a yau Litinin, ta ce an samu ƙaruwar ne sakamakon canji da aka samu a farashin kayan abinci.
Rahoton ya kuma nuna cewa farashin kayan abinci ya tashi zuwa kashi 22.25 wanda ya zarce kashi 20.60 da aka samu a watan Yunin 2022.
A ranar Alhamis 13 ga watan Yuli, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana dokar ta-ɓaci kan samar da abinci a matsayin martani ga hauhawar farashin abinci a ƙasar.
A ‘yan kwanakin nan, ‘yan Najeriya na kokawa kan hauhawar farashin kayan abinci, kuma a yayin da ake ci gaba da kokawa, gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur, lamarin da ya ƙara jefa masu karamin karfi cikin mawuyacin hali.