Hukumar kare jama'a ta ƙasar, ta ce wata motar bas ce ɗauke da fasinjoji da garu da wata mota kafin su kama da wuta.
An kuma ruwaito cewa wasu mutum 12 ne suka samu raunuka.
Ba a dai kai ga gano waɗanda lamarin ya rutsa da su ba, amma lardin na Tamanrasset yana kusa da ƙasashen Niger da Mali, kuma wuri ne da ƴan cirani da yankin sahara na Afrika ke amfani da shi wajen tsallakawa zuwa Turai.