Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Juma'a mai ɗauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a na hukumar Nkechi Isa, ya ce hukumar na gargaɗin ne bayan da hukumar kula da yanayi ta ƙasar ta yi hasashen samun ruwan sama mai ƙarfin gaske haɗe da iska da ambaliya da zaizayewar ƙasa a wasu sassan jihohin Katsina da Kano da Bauci da Plateau da Taraba da kuma Abujan
Hukumar kula da yanayi ta kasar NiMET ta yi hasashen cewa za a samu ambaliya ruwa tare da batsewar koguna da iska mai ƙarfi, da zaizaiyewar ƙasa da walkiya da kuma tsawa.
Hukumar ta NiMET ta yi kira a sauya matsugunai ga al'umomin da suke cikin hatsarin fuskantar ambaliyar, wadda za ta iya lalata dukiyoyi tare da haifar da cutattuka.
Babban daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin Abuja Dakta Abbas Idriss ya ce hukumar ta sanya jami'anta cikin shirin ko-ta-kwana don fuskantar matsalar.
Haka kuma ya yi kira ga mazauna birnin da su riƙa la'akari da gargadin da hukumar ta fitar, tare da kaucewa yin tuƙi ko tafiya a ƙafa a lokacin da ake tsaka da ruwan sama, tare da kauce wa titunan da ruwan zai iya mamayewa.
Ya kuma nemi jama'a da su yi gaggawar tuntuɓar hukumar idan suna buƙatar taimakon gaggawa daga gareta.