Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusif ne ya bayyana hakan lokacin da wata kungiyar kwararru masu bincike da nazari akan sauyin yanayi da makamashi suka kawo ziyara fadar gwamnatin kano.
Gwamnan Wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin kano Dr Baffa Bichi yace gwamnatin su ta himmatu matuka wajen dawo da darajar masana'antun jihar wadanda suka durkushe ta hanyar Samar da ingantacciyar wutar lantarki domin gudanar da ayyukansu.
Tun da farko da yake jawabinsa Shugaban rukunin kamfanonin Lee dake najeriya Kuma shugaban hukumar kwashe shara ta jihar nan Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya bayyana cewa daga cikin abin takaicin da yake damunsu shine yadda kamfanonin 'yan asalin jihar Kano suke yin kaura ya zuwa wasu jihohin.