Gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa kwamiti da zai bibiyi kudaden da gwamnatin baya ta kashe ba bisa kai'da ba a karshe wa'adin mulkin, wanda Adadinsu ya kai biliyan goma 10.
Wadanda aka kafa a kwamitin sun hada da:
1. Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsare, Hon. Musa Sulaiman Shanono
2. Kwamishinan Shari'a, Barrister Haruna Isa Dederi.
3. Kwamishinan Ilimi, Hon. Umar Haruna Doguwa.
4. Kwamishinan Noma, Dr Danjuma Mahmood.
5. Sakataren Gwamnati, Dr Abdullahi Baffa Bichi.
6. Ahmad Garba Sale a matsayin Magatakardar Kwamitin.
Gwamnan ya kuma umarcesu dasu fara gudanar da aikin nan ta ke.