Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton dawo da shirin auren zawarawa, wanda za'a fara bayan kammala harkokin aikin Hajjin bana.
Hakan na kunshe cikin sanarwar da majalisar zartarwar jihar ta aiko mana, bayan zama da tayi a ranar Laraba, karkashin jagorancin gwamna, Alh Abba Kabir Yusuf.