Shugaban hukumar ta jihar Kano Barr Muhuyi Magaji Rimin Gado wanda yace baya bindiddigi akan batan dabo da motocin sukayi, zuwa yanzu sunfara samun nasarar kwato su.
Dayake jawabi a yayin ziyarar gani da ido, kwamishinan sufuri na Jihar Kano Engr Muhammad Digol ya nuna takaicinsa biya babakere da tsohowar gwamnatin Kano tayi, wajen sayar da kadarorin al'ummar Kano ba bisa ka'ida,
Sai dai bayan sayar da motocin toni aka canja musu kammani da fenti, kuma ake harkokin kasuwanci dasu akan titina daban-daban, I zuwa yanzu gwamnati taci alwashin gyara motocin domin mayar dasu hukumarsu ta asali dancigaba da gudanar da ayyuka dasu.