Gwamnan ya ce matakin zai fara aiki ne daga zangon karatu mai zuwa, domin rage raÉ—aÉ—in cire tallafin fetur da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi.
Matakin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Emmanuel Bello ya fitar.
Gwamnan ya jaddada cewa hakkin gwamnati ne ta dauki nauyin ilimi a matakin farko, saboda haka bai kamata dalibai su rika biyan ko sisi ba.
Ya ce baya ga cika alkawarin neman zabe, wahalhalun da aka samu na cire tallafin man fetur sun sanya ya zama wajibi a É—auki wannan mataki.
A baya dai gwamnan ya rage kudaden shiga jami’o’i da kashi 50 cikin 100 domin rage wahalhalun da al'umma ke fuskanta.