Jakadan China a Najeriya ya yaba wa ziyarar ayarin jiragen sojin ruwan ta kwana biyar a matsayin wani muhimmin lamari cikin alaƙar ƙasashen biyu, kuma rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyarta na aiki tare da China don magance barazanar tsaron teku da tabbatar da kwanciyar hankali a Mashigin Tekun Guinea, in ji wata sanarwa daga ofishin jakadancin China.
China dai ta daɗe tana ƙoƙarin bunƙasa faɗa-a-jinta a Afirka.
Jirgin wargaza hare-haren da kuma wani jirgin yaƙi mai rakiya da ake kira 'Sanya' tare da wani jirgin dakon kaya, Weishanhu sun isa daf da gaɓar tekun Lagos a cewar wata sanarwa daga sojin ruwan Najeriya.
Yankin Afirka ta Yamma mai arziƙin man fetur, muhimmin yanki ne da ke fitar da ɗanyen mai a duniya.
Yankin, musamman ma dai Angola da Najeriya na cikin manyan ƙasashe masu samar da man fetur ga China. Sannan wani babban kamfanin haƙar man fetur na China CNOOC Ltd kuma yana aikin fito da man fetur daga can ƙarƙashin tekun gaɓar Najeriya.
A watan Janairu ne, Najeriya ta buɗe wata tashar teku mai zurfi ta dala biliyan ɗaya da China ta gina a Legas. Sabuwar tashar jiragen ruwan ta Lekki, na ɗaya daga cikin tashoshin ruwa mafi girma a yankin, kuma kamfanonin China Harbour Engineering Co. mallakar gwamnatin China da Tolaram Group na ƙasar Singapore na da jarin kashi 75% a tashar.
Akwai raɗe-raɗin cewa ƙasashen yankin Tekun Guinea na iya bai wa sojojin China wuri don kafa sansaninsu.
A bara, jami'an tsaron Amurka sun bayyana damuwar cewa irin wannan sansani mai yiwuwa a ƙasar Equatorial Guinea na iya barazana ga tsaron Amurka.
A shekara ta 2017, China ta buɗe sansanin sojojin ruwan ta na farko a wajen ƙasar cikin Djibouti ɗaya daga cikin cibiyoyi mafiu muhimmanci na hada-hadar teku, abin da ya tsananta damuwar cewa hukumomin Beijing na iya kafa ƙarin sansanonin a yankin, daidai lokacin da sojojinta ke daɗa bunƙasa don gudanar da aikace-aikace a wurare masu nisan dubban kilomitoci daga gida.