Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Juma'a, yayin da ake wani aikin horo.
Daraktan hulda da jama’a da yaÉ—a labarai na rundunar sojin sama ta Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Ya ce matukan jirgi biyu na samun kulawa a asibitin sojojin sama da ke brinin Makurdi.
“An yi sa’a, matukan jirgin biyu da ke cikin jirgin sun tsira daga hatsarin bayan da suka yi nasarar ficewa daga cikin jirgin. Bugu da kari, babu asarar rayuka ko asarar dukiya a inda hatsarin ya faru.
Ya ƙara da cewa a halin da ake ciki, babban hafsan sojin sama na Najeriya, Air Vice Marshal Hassan Abubakar, ya kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin hatsarin nan take