Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da nadin mai shari'a, Jostis Dije Aboki, a matsayin mace ta farko Babbar Jojin jihar Kano.
Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ne ya gabatar da sunan Mai Shari'a Dije Aboki ga majalisar don tantancewa da tabbatar da ita a matsayin Babbar Jojin.