Wata kotu a Jumhoriyar demokradiyar Kongo ta yanke wa wasu mutane 21 da aka kama da laifin satar mutane hukuncin ɗaurin shekara 21 a gidan yari.
Mai shari'a Evariste Ewalaseno ya yanke hukuncin ne a ranar Juma'a, bayan gomman mutane da abin ya shafa sun bayyana a gaban kotun don bayar da shaida.
Shaidun sun ba da labarin yadda ’yan kungiyar suka yi awon gaba da wasu daga cikin su bayan da aka yi garkuwa da su a cikin motocin tasi a cikin birnin kinshasa.
An kammala shari'ar ne bayan kusan kwana guda na sauraren koken-koken jama'a.
Kotun ta bude zama ne a ranar Laraba da yamma kuma ta bayar da umarnin kama su nan take domin kai su gidan yari, bayan yanke hukuncin na yau.
A cikin bukatun da ya gabatar a gaban kotu, mai gabatar da ƙara Edmond Isova, ya nemi a yanke wa masu laifin hukuncin kisa.
Kotun ta bayar da umarnin biyan diyya daga dala 10,000 zuwa dala 20,000 ga mutane 23 da abin ya shafa, ciki har da Serge Movili Mazami, wani fitaccen makaɗi wanda aka fi sani da Celeo Scram, wanda aka yi masa fashi.
Kotun ta ce masu laifin na iya daukaka kara kan hukuncin.
Jama’a da dama ne suka halarci zaman domin sanya ido, duk da cewa an yanke hukuncin ne da maraicen yau Juma’a.
Jama'a sun hallara don jinjina wa kotun kuma hukuncin da aka yanke ya samu karɓuwa ga mazauna Kinshasa, waɗanda da dama suka kasance cikin fargabar shiga tasi.
Wadanda aka yanke wa hukuncin dai kashi na farko ne na mutane 27 da ake tuhuma da laifin gudanar da ayyukan a Kinshasa babban birnin kasar.