Amincewar ta biyo bayan tantance hafsoshin da aka yi a zauren majalisar ranar Alhamis.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ce a lokacin tantancewar, wadda aka yi a asirce, hafsoshin sojin sun amsa tambayoyi kan lamurran da suka shafi tsaro da kuma halin da ƙasar ke ciki.
A ranar Litinin, Shugaban Tinubu ya aika wa majalisar da wata takarda yana buƙatar amincewa kan naɗin da ya yi wa manyan hafsoshin.
Manyan hafsoshin da aka amince da naɗin nasu su ne:
- Manjo-Janar C.G Musa (Hafsan hafsoshin dakarun Najeriya)
- Manj-Janar T. A Lagbaja (Babban hafsan mayaƙan ƙasa)
- Rear Admiral E. A Ogalla (Babban hafsan mayaƙan ruwa)
- AVM H. B Abubakar (Babban hafsan mayaƙan sama)
- IGP Kayode Agbetokun (Mai riƙon muƙamin Sufeta-Janar na ƴan sanda)
- Manjo-Janar EPA Unidianye (Shugaban Hukumar Tattara bayanan sirri na tsaro)