Kudurin neman yi wa dokar kwaskwarima ya haramta bayar da tallafin kudi domin harkokin ‘yan luwadi da madigo.
Dama dai an haramta wa maza neman junansu a Ghana, to amma sabon kudirin dokar ya hada da haramta wa mace neman yar uwarta.
‘Yan majalisar daga jam’iyyu daban daban sun tafka muhawara kan rahoton wani kwamiti da aka ba shi aikin yi wa kudurin kwaskwarima.
Kungiyoyin ‘yan majalisar wakilai suma sun goyi bayan gyare-gyaren, za kuma a sake nazarin gyare-gyaren kafin su zama doka.
Wata yar majalisa daya tilo da ta nuna dan sassauci a fili ga masu luwadi da madigo to fuskanci sowa har sai da ta mika wuya.
A watan Agustan 2021 ne aka fara gabatar da kudurin dokar hana auren jinsi a zauren majalisar Ghana, sai dai an rika fuskantar mummunar suka gida da waje.
An shigar da kararraki da dama a gaban kotunan kasar da nufin kalubalantar kudurin.
Wadanda suke adawa da shi sun ce idan ya zama doka zai tauye wa 'yan luwadi da madigo yancinsu da kundin tsarin mulki ya ba su.
Sai dai masu goyon bayan kudirin sun ce zai taimaka wajen kiyaye kyakkyawan tsarin iyali na al’ummar Ghana.
Majalisar za ta sake bibiyar kudirin kafin amincewa da shi don zama doka.