Pakistan ce ta gabatar da ƙudurin, inda ta ce gwamnatoci na bari ana wulakanta littafi mai tsarki na mabiya addinin musulunci.
An bukaci kasashe da su samar da dokoki waɗanda za su hana faruwar hakan, da kuma hukunta waɗanda aka samu da irin wannan laifi.
Ƙasashen dai ƙasashen yamma, ciki har da Amurka da Birtaniya da kuma kasashen Kungiyar Tarayyar Turai suka nuna adawarsu ga matsayar.
Sun ce matakin ya yi kutse ga ƴancin fadar albarkacin baki.