‘Yan majalisar sun nuna damuwarsu kan yadda hukumar jarabawar ta gaza nuna dattaku kan lamarin da ya shafi karamar yarinya ta hanyar janye sakamakon jarabawarta tare da dakatar da ita na tsawon shekaru uku.
Sun ce yana yiwuwa akwai hannun wani a cikin lamarin.
Daga nan ne majalisar ta kafa kwamitin da zai binciki lamarin tare da neman hukumar JAMB da ta dakatar da zartar da hukunci har sai majalisar ta kammala bincikenta.
A ranar Lahadin da ta gabata ne hukumar ta JAMB ta zargi dalibar da kirkirar sakamakon bogi a jarabawar ta bana.