Tajedeen ya ce ya zama wajibi a sama wa sarakunan gargajiyar matsayin a kundin tsarin mulkin ƙasar ganin irin rawar da suke takawa a cikin al'umma.
Kakakin Majalisar Wakilan na wannan jawabi ne a lokacin wata ziyara da ya kai fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau Alh. Dakta Nuhu Bamalli.
Hon Tajedeen wanda ke da matsayin sarautar Iyan Zazzau, na wakiltar mazaɓar zariya a Majalisar Wakilan ƙasar.
A lokacin ziyarar ya bayyana irin kima da martabar da sarautar gargajiya ke da shi, a don haka ne ya yi kira da a samar wa sarakunan gargajiya matsayi a kundin tsarin mulkin kasar.
“Na tuna lokacin da muka saurarin ra'ayoyin jama'a kan yi wa kundi tsari mulkin gyaran fuska a shiyoyin Æ™asar nan daban-dabn shekara uku da suka gabata, kun gabatar da buÆ™atar samar wa sarakunan gargajiya matsayi cikin kundin tsarin mulki''.
''To ina mai tabbatar muku cewa a yanzu kuna da damar samun haka. A matsayina na ɗa gareku kuma nake jagorantar Majalisar Wakilai, za mu duba wannan ƙuduri domin samar wa sarakunanmu matsayi cikin kundin tsarin mulkin ƙasarmu'', kamar yadda mataimaki na musamman ga kakakin majalisar Musa Krishi, ya bayyana cikin sanarwar da ya fitar.
Daga ƙarshe ya kiran samun haɗin kan sarakun gargajiya musamman na yankin arewacin Najeriya domin tabbatar da wannan yunƙuri, tare da neman shawarar sarakunan gargajiyar don samun nasarar sauke nauyin da ke rataye a wuyansa na jagorancin majalisa.
A nasa ɓangare sarkin Zazzau ya ce, da yawa daga cikin 'yan siyasar ƙasar, da zarar sun ci zaɓe sukan manta da sarakunan gargajiya.