Wani matashi ɗan shekara 32, mai suna Samson Sikiru,ya shaƙe mahaifiyarsa har ta mutu a garin Ijebu Ode da ke jihar Ogun.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Omotola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ana dai zargin matashin da tu'ammali da ƙwayoyi.
Kanin wanda ake zargi da kashe mahaifiyar tasu, wanda yake aikin gadi, shi ya sanarwa makwaɓtansu abin da ke faruwa lokacin da ya dawo ya samu gawar mahaifiyarsu a kwance.
Samson wanda ya kasance ba ya gida na tsawon shekaru, ya dawo ne domin yin bikin babbar Sallah tare da mahaifiyarsa makonni biyu da suka wuce.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa an kama matashin ne bayan da makwaɓtansu suka gano cewa shi ya kashe mahaifiyar tasa, inda daga nan aka miƙa shi hannun ƴan sanda.
Kakakin ƴan sandan jihar ta Ogun, Omotola Odutola ta ce matashin yana da lalura ta kwakwalwa.
Ta kuma ce an kasance ana ɗaure lokuta da dama domin kada ya ji wa kansa ko mutane ciwo.