Jihohi da dama a Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalar cin zarafin yara tare da yi masu fyaɗe, wanda mutane da yawa suka bayyana a matsayin annoba.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya shaida wa manema labarai cewa, hukumomi sun damu da yadda ake samun ƙaruwar masu lalata da ƙanann yara a jihar.
"A halin yanzu ana kan binciken kusan ƙararraki 83, wanda ke nuna ƙudurin rundunar na hukunta duk wani abu da ya shafi irirn wadannan laifukan a jihar," in ji shi.
Mista Hundeyin ya bayyana cewa a tsakanin watan Afrilu zuwa 14 ga watan Yuni an samu rahoton aikata laifukan fyaɗe da kuma laifuka 56 na rikicin cikin gida.
Ya kuma bayyana cewa an gurfanar da mutane 99 a gaban kotu.
A Najeriya laifukan da suka shafi lalata da kananan yara na neman su kai matakan tashin hankali.
Ɗaruruwan abubuwan da suka faru ba a bayar da rahotonsu saboda cin hanci da rashawa da ke yaɗuwa, da ƙyamar da ake nunawa waɗanda abin ya shafa da kuma tafiyar hawainiyar shari'a.
Masu fafutuka na ci gaba da kokawa kan yadda ake cigaba da cin zarafin yara da kuma yi masu fyade, da kuma ƙarancin hukuncin da ake yi wa masu aikata irin waɗannan laifukan a ƙasar.
Sun daɗe suna matsawa kan daukar tsauraran matakai don magance matsalar.