Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada cewa za ta cimma kudirinta na kawo ƙarshen yaɗuwar cutar HIV zuwa shekarar 2030.
Sai dai ta yi gargaɗin cewa rashin kuɗin aiki da kuma nuna tsangwama ga masu cutar yana kawo cikas ga aikin.
Kididdigar da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ta nuna cewa mutum miliyan 39 ne ke ɗauke da cutar HIV a duniya.
Kuma akalla mutum miliyan 30 daga cikinsu ne ke karɓar maganin da ke rage kaifin cutar.
Majalisar Dinkin Duniyar ta kuma ce akwai buƙatar samun ƙarin kuɗin yaƙi da cutar, da kuma mayar da hankali daga bangaren gwamnatoci, idan har ana son kawar da ita.