Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta hana gwamnatin jihar Kano da jami’anta da ƴansanda da ƴansandan farin kaya da dai sauransu daga kama tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje da duk wasu makimusantan sa.
Alkalin kotun, Mai shari’a A. M. Liman, a cikin takardar umarnin, mai dauke da kwanan wata 6 ga Yuli 2023 ya amsa wa masu shigar da korafin bukatar su.
Umurnin ta ce: “Wadanda ake kara ko su da kansu, ko kuma ta hanyar jami’ansu,jami’ansu, jami’an tsaron su, masu zaman kansu ko wani mutum ko gungun mutane kar su musgunawa, tsoratarwa, gayyata, barazanar kamawa, kamawa ko tsare wanda ya shigar da korafi, ko 'ya'ya ko wani daga cikin danginsa, ko duk wanda aka nada wanda ya yi aiki a karkashin kulawar mai korafi ko kuma ya karbe kadarorin mai korafi da karfi ko 'ya'yansa ko wani daga cikin danginsa, ko duk wanda aka nada wanda ya yi aiki a karkashin gwamnatin mai korafi har sai an yanke hukunci a kan neman hanawar.
"Cewa umarnin wucin gadi zai yi aiki har zuwa lokacin da za a saurari ƙorafin da aka shigar a kan tauye ƴancin ɗan adam zuwa ranar 14 ga Yuli, 2023.
Wadanda aka baiwa umarnin za a ba su kundin umarnin sa’o’i 36 daga yau,” in ji alkalin.