Lamarin ya rutsa da mutum 17 waÉ—anda suka haÉ—a da maza 12 da mata guda biyu da kuma wasu yara guda uku.
Mutanen da suka mutu sun kunshi maza guda bakwai da mace guda É—aya da kuma yara biyu.
Hatsarin ya afku a ranar yammacin ranar Alhamis, inda wasu motoci guda uku suka garu, abin da kuma aka danganta faruwarsa da gudu fiye da kima da kuma kokarin wucewa da direbobin motocin suka yi.
Babban kwamandan hukumar kiyaye haÉ—ura ta jihar, Fredrick Ade Ogidan ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka garzaya da waÉ—anda suka jikkata zuwa asibiti domin ba su kulawar gaggawa, yayin da aka kai waÉ—anda suka mutu kuma É—akin ajiyar gawawwaki na asibitin koyarwa na Jami'ar jihar da ke Ilorin.