Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa kan tashe-tashen hankula na baya-bayan nan da ake samu a jihar Filato.
A cikin wata sanarwa da Tinubu ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Dele Alake, shugaban ya yi alla-wadai da rikicin wanda ya janyo kashe-kashen rayuka a ƙaramar hukumar Mangu da kuma wasu kashe-kashen a jihar Benue.
Ya ce "Ana buƙatar haƙuri da yafiya kan kuskuren da wani ya yi matuƙara ana son samar da ingantacciyar al'umma."
Ya ƙara da cewa "Abin takaici ne yadda jaririya mai watanni takwas a duniya ta rasa ranta sanadiyyar rikicin da ba ta san komai ba a kai a ƙauyen Farin Lamba da ke jihar Filato."
Ya buƙaci shugabannin al'umma da ƙungiyoyin Jama'atu Nasril Islam da CAN su haɗa hannu domin samar da mafita ga lamarin.
Shugaban ya kuma umarci jjami'an tsaro da su zaƙulo duk waɗanda ke da hannu a kashe-kashen domin fuskantar hukunci.
Sannan ya buƙaci gwamnatin jihar ta Filato da ta kai ɗaukin gaugawa ga waɗanda lamarin ya rutsa da su.
A farkon wannan mako ne hukumomi suka ayyana dokar hana zirga-zirga a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato bayan tashe-tashen hankula waɗanda suka yi sanadin rayukan mutane da dama.