Gargaɗin na zuwa ne bayan da aka gano ruwa mai yawa cikin tankin man ɗaya daga cikin jiragen kamfanin Max Air, wanda ya mallaki Boeing 737 da aka dakatar da tashinsa cikin makon da ya gabata.
Rahotonni sun ambato Darakta Janar na hukumar sufurin jiragen saman ta Najeriya Kaftin Musa Nuhu na cewa hukumar na gudanar da bincike kan wasu kamfanonin da ke samar da man jirgin, domin gano yadda man ya haɗu da ruwan.
Ya kara da cewa ''muna bincike game da komai, mun gano cewa wannan jirgin ya sha mai a tasoshin jiragen Legas da Kano da kuma Abuja. Dan haka muna sa ran samun rahoton bincike game da wadannan tasoshin shan man, kuma duk tashar da muka samu da laifin za mu dakatar da ita har sai an magance matsalar''.
''Daya daga cikin manyan matakan kariya a hukumarmu shi ne tabbatar da ingancin man jirgi tare da bin matakan tsaftace shi'', in ji shi.
Daraktan ya ƙara da cewa a baya an samu hatsarin jirage sakamakon gurɓacewar man da suke amfani da shi, wanda ke yin lahani ga injin jirgin, kuma ruwa na daga cikin manyan abubuwan da ke gurɓata man jirgi.
Haka kuma hukumar ta yi kira ga ma'aikatanta da ke tasoshin man jiragen da su riƙa auna man tare da gwada ingancinsa kafin su bari jiragen su sha man.