Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya NDLE ta ce tana bincike game da wani rikici da ya kai ga harbe-harbe a lokacin da jami’anta suka kai samame kan wata dabar masu sayar da miyagun ƙwayoyi a unguwar Okpanam da ke Asaba a jihar Delta.
Lamarin da ya sa harsashi ya samu wani matashi, abin da kuma ya yi sanadiyyar mutuwarsa a asibiti a lokacin da ake yi masa maganai.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Asabar, shugaban hukumar Burgejiya Janar Buba Marwa mai ritaya ya ce ya kafa wani kwamiti mai ƙarfi daga shalkwatar hukumar da ke Abuja tare da tura shi zuwa jihar Delta don gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin gaskiyar abin da ya faru.
Rahoton binciken farko ya nuna cewa ‘’A ranar Alhamis 13 ga watan Yuli, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma Jami’an hukumar NDLEA suka ƙaddamar da wani samame bayan samun bayanan sirri kan wata dabar manyan dilolin ƙwaya da ke unguwar Okpanam na jihar Delta, inda a yayin samamen aka samu yamutsi tsakanin jami’anmu da gungun masu laifin wadanda ke cikin wata mota ƙirar Toyota Camry, inda suka harbi ɗaya daga cikin jami’anmu wanda yanzu haka ke cikin mawuyacin hali a asibiti’’
‘’A ƙoƙarin hana motar guduwa ne wani jami’inmu ya yi yunƙurin harbin tayar motar’’.
Sanarwar ta ce a yayin da aka ɗauki jami’in hukumar zuwa asibiti, sai jami’an suka samu labarin cewa harsashin da jami’in nasu ya harbi tayar motar ya samu wani matashi, inda jami’an hukumar suka yi gaggawar gano mahaifinsa, tare da bin sa zuwa asibiti domin taimaka masa, sai dai matashin ya mutu a lokacin da ake yi masa magani.
“Muna tattaunawa da iyalansa domin ba su duk taimakon da suke bukata. Yayin da muke gudanar da bincike, muna masu tabbatar wa iyalan matashin da sauran al’ummar gari cewa za mu yi ƙoƙarin gano ainihin abin da ya faru domin ɗaukar matakin da ya dace’’, in ji sanarwar.