Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero ya fitar ranar Talata.
Sanarwar ta ce, "Shawarar biyan naira 8,000 ga magidanta miliyan 12 mafiya talauci a Najeriya tsawon wata shida cin mutunci ne da kuma ba'a ga haƙuri da imani da muke da shi a kan tattaunawa da gwamnati."
"Rashin tunani ne gwamnatin da ta haddasa tsananin wahala a kan mutane cikin ƙasa da wata biyu da hawanta mulki, sannan ta zo ta kawo wani ƙuduri wanda ƙarara zai saka wa masu kuɗi da ke riƙe da muƙaman gwamnati, ba tare da duba halin da talakawa ke ciki ba."
"Abin da hakan ke nufi shi ne gwamnati na neman hanyoyin da za ta sace dukiyar talakawa 'yan Najeriya, su kuma masu kuɗi su ƙara kuɗancewa."
NLC ta ce ba za a lamunci waɗannan ƙudurori ga ma'aikatan Najeriya ba kuma matakin ya fi kama da kama-karya don haka ya saɓa da tsarin dimokraɗiyya.
"Muna nanata cewa ba mu da ƙwarin gwiwa kan hanyar da aka bi aka tattara bayanan da ba sa canzawa na gidajen mutanen da suka fi talauci su miliyan 12, sannan ba mu da ƙwarin gwiwa a kan tsare-tsare da za su bi wajen raba wannan kuɗi."