Rohotan da Daily Trust ta rawaito na cewa, Mai Martaba Sarkin Minna na cikin fadar a lokacin da barayin suka ka yi ta harbe-harben bindiga domin razana jama'a, kuma daga bisani sun yi awon gaba da kudaden da ba a bayyana adadinsu ba.
An dai ce kudaden mallakin Masarautar ce ta Minna, yayin da aka garzaya da dogaran da aka harba babban asibiti don yi musu magani.
Wani mutun da lamarin ya faru a gaban idonsa da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, 'yan fashin da makami sun fi karfin 'yan bangar da aka girke suna tsaron fadar.