''Da yawa ana ta raÉ—e-raÉ—in cewa shugabannin makarantu wato principal sun cefanar da filayen makarantu wanda ba haka abun yake ba kuma ba gaskiya bane face raÉ—e-raÉ—i dake yaÉ—uwa a cikin al'umma ta hanyar yaÉ—a farfaganda.
Duk wasu shugabannin makarantu (Principal) basu da dama ta kusa ko ta nesa na su cefanar da filayen makarantun da suke shugabanta illa iyaka duk lokacin da gwamnati tayi niyyar cefanar da makamantan wannan gurare a makarantu ta kan kira shugaban makaranta ta faɗi abunda take son yi da guri tare da umartar shi/ita kan su bada haɗin kai yayin da aka zo don gudanar da aikin yanka fili ko gini da sauran su'' inji shi. ya kuma ƙara da cewa
"babu wani shugaban makaranta da zai yi farin ciki don an cefanar da filin makarantar da yake shugabanta musamman ma idan ba makarantar ce zata amfana da wannan gini da za'ayi domin baiwa wasu haya ko don yin kasuwanci, haka xaluka (Principal) ma'aikaci ne kamar kowane ma'aikacin gwamnati saboda haka baida dama ko ta kusa ko ta nesa na ya cefanar da filin makaranta da sauran abubuwan makaranta domin mallakin gwamnati ne kuma idan yayi hakan ya sabawa doka kuma za tayi hukunci a kansa''
A ƙarshe ya miƙa saƙon godiya da jinjina ga gwamnatin Engr Abba Kabir Yusuf bisa baiwa ƴan fensho haƙƙunan su musamman waɗanda sukai aikin koyarwa, muna kuma da yaƙinin wannan gwamnatin tazo ne da niyyar gyara da kuma kawo sabbin tsare-tsaren da zasu amfanar da al'ummar jihar kano da kewaye.