Dakarun sojin Najeriya sun ce sun ceto mutum 40 da ƴan bindiga suka garkuwa da su a jihar Zamfara.
Dakarun da ke aiki ƙarƙashin rundunar Operation Hadarin Daji sun samu nasarar ceto mutanen ne a karamar hukumar Bukkuyum na jihar.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa sojojin sun samu nasarar ce bayan samun bayanan sirri da ke cewa ƴan bindigar sun yi garkuwa da mutanen da ba a san adadinsu ba a ƙauyen Kyairu da Alkama da ke karamar hukumar ta Bukkuyum.
Bayan nan ne sojojin suka tasamma garin da nufin kai samame domin ƙwato mutanen da ke hannun ƴan bindigar a ranar Talata.
Sai dai sojojin sun yi bata kashi da ƴan bindigar na wasu sa'o'i kafin su fi karfinsu da tilasta musu tserewa da kuma barin mutanen da suka yi garkuwa da su.
Mutanen da aka ceto ɗin da suka kai 40 tuni suka haɗu da iyalansu yayin da aka miƙa goma daga cikinsu kuma ga hannun Sarkin Gwashi domin haɗa su da iyalansu.