Cikin wani sakon Twitter da rundunar sojin ƙasan Najeriya ta wallafa, ta ce an ƙaddamar da rundunar ne domin magance tashe-tashen hankulan da ake yawan samu, a ƙaramar hukumar, lamarin da ke ƙara haifar da taɓarɓarewar tsaro a yankin.
Yayin da yake jawabi ga dakarun rundunar, a lokacin ƙaddamarwar, babban hafsan soji ƙasa na Najeriyar ya yi kira a gare su da sun kawar da duka wani nau'in barazanar tsaro da yankin ke fuskanta da ma jihar Plateau baki-ɗaya.
Manjo Janar Lagbaja ya ce dakarun su tabbatar sun yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da tsaron lafiyar mazauna yankin, ta hanyar gaggauta kai ɗauki a duk inda aka buƙace su.
Ya kuma sake nanata wa sojojin irin ƙwarin gwiwar da al'umma gari ke da shi a kansu.
Haka kuma babban hafsan sojin ƙasar ya gana da masu ruwa-da-tsaki na ƙaramar hukumar, inda ya yi kira a gare su, da su nuna kishi wajen maido da zaman lafiya a ƙaramar hukumar, wani abu da ya kira ''Babban aikin maido da zaman lafiya a Mangu''.
Yana mai cewa babu wanda zai kai al'ummar garin tare da iyalansu jin daɗi, idan aka samu samu zaman lafiya a yankin.
A baya-bayan nan dai an samu rahotonnin tashe-tashen hankula a garin na Mangu.
Jihar Plateau na daga cikin jihohin Najeriya da ke yawan fama da rikice-rikice masu alaƙa da addini da ƙabilanci da na manoma da makiyaya.