Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Hadarin Daji sun samu nasarar kashe wasu ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Dakarun sojin Najeriyar sun ce sun samu nasarar ce a ranar 20 ga watan Yuli bayan kai samame maɓoyar ƴan bindigar wanda hakan na cikin zimmar sabon hafsan sojin ƙasa Manjo Janar T. A Lagbaja na ganin an dawo da zaman lafiya a jihar da kuma yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Sojojin sun kuma samu nasarar tarwatsa sansanonin ƴan bindigar da dama a ƙauyukan Mutuwa da Guda tudu da Kawar da Dantayawa da Gidan Kare da Mahuta da kuma Gyado da ke jihohin Zamfara da Skoto.
Sai dai an yi ta artabu tsakanin sojojin da kuma ƴan bindigar, inda daga bisani sojojin suka fi karfin ƴan bindigar da kuma samun nasara a kansu.
Sun kuma samu nasarar ƙwato bindiga da harsasai da kuma babura huɗu daga hannun ƴan bindigar.
Haka ma, a irin wannan samame da sojojin suka kai karamar hukumar Maradun, sun samu nasarar kashe ƴan bindiga huɗu da hana su shiga ƙauyen yayin da wasu suka tsere da raunukan bindiga.