Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ta hannun daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu.
Sanarwar ta ce rundunar ta ɗauki mataki ne bayan tattara bayanan sirri, a kan hanyar Ajilete zuwa Owode a karamar hukumar Yewa ta Arewa a jihar Ogun a ranar Asabar, 15 ga Yuli, 2023.
Janar Nwachukwu ya ce a yayin farmakin sojojin sun gano wata babbar mota wadda ke jigilar alburusai masu yawa da ke kan hanyarta zuwa jihar Anambra.
Dakarun sun yi gaggawar cafke wadanda ake zargi da hannu a yunkurin fasa kwaurin.
A halin yanzu dai dukkan mutanen na hannun jami'an tsaro, yayin da ake ci gaba da bincike.
Binciken farko da aka yi ya nuna cewa an boye alburusai a cikin motar, ta yadda ba za a iya ganewa ba.