A wani taro na majalisar ƙoli ta shari'a ta ƙasar, Montazeri ya ce Ma'aikatar Lafiya ta aike da shari'o'i 119 da suka shafi zubara da ciki, sai dai ya ce an dunkule su zuwa 45.
A dokar Iran zubar da ciki haramun ne, kasancewar doka ta tanadi batun ƙara yawan al'ummar ƙasar.
Haramta zubar da ciki ya tursasa wa mata bin ɓarauniyar hanya a ƙoƙarinsu na zubar da cikin, lamarin da ke sanya rayukansu cikin haɗari.