Dakarun waɗanda ke aiki ƙarƙashin shirin wanzar da zaman lafiya na ƙasashen ƙungiyar ECOWAS sun yi wa shugaban faretin ban girma.
Shugaban na tare da babban kwamadan dakarun wanzar da zaman lafiya na ƙasashen ECOWA Burgediya Janar Al-hassan Grema, da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu da babban sakatare a ma'aikatar harkokin kasashen waje Ambassador Adamu Lamuwa.Sauran 'yan tawagar shugaban ƙasar sun haɗar da tsoffin gwamnonin jihohin Jigawa da Kebbi da Kano.